Isa ga babban shafi
Najeriya

Kamfanin Arik Air zai kalubalanci gwamnatin Najeriya a kotu

Hukumar gudanarwar kamfanin jiragen sama na Arik ta ce zata garzaya kotu domin kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na karbe ragamar jagorancin kamfanin.

Jirgin sama na kamfanin Arik Air
Jirgin sama na kamfanin Arik Air Laurent Errera/Wikimedia Commons
Talla

Mataimakin shugaban kamfanin Ado Sunusi ya sanar da yanke shawarar, yayin wani taron manema labarai da ya kira.

A dai ranar Alhamis din hukumar da ke lura da kadarorin gwamnati ta Najeriya AMCON ta karbe ragamar jagorancin kamfanin jiragen sama na Arik Air, saboda tarin basussukan da ake binsa, a ciki da kuma wajen Najeriyar.

Yayin taron manema labaran mataimakin shugaban kamfanin, Ado Sunusi ya ce hukumar ta AMCON ta gabatar musu da takardar kotu da ke bawa hukumar ikon karbe kamfanin daga hukumar gudanarwarsa.

To sai dai, kuma Sunusi ya ce duk da cewa sun bi umarnin, hakan ba zai hana suma su garzaya wata kotun ba domin neman a soke umarnin da ta farko ta bada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.