Isa ga babban shafi
Najeriya

Jirgin saman Arik ya koma bakin aiki

Kamfanin jirgin sama na Arik da ke Najeriya ya sanar da janye matakin da ya dauka na dakatar da zirga-zirga.

Kamfanin jiragen sama na Arik ya koma bakin aiki
Kamfanin jiragen sama na Arik ya koma bakin aiki Crédit : Biggerben/Wimedia Commons
Talla

A jiya ne dai, manajan sashen hulda da jama’a na kamfanin, Olabanji Ola ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen saboda matsalar insora, wadda zai an magance ta kafin jiragen su samu izinin tashi.

Sai dai daga baya, Mr. Ola ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sun gyara matsalar ta insora, abinda ya bai wa jiragen damar komawa aiki, inda za su fara jigila tsakanin Abuja da Port Harcourt.

Shugaban kamfanin Dr. Michael Arumemi-Ikhide ya bai wa fasinjoji hakuri game da daukan matakin jingine aiki, abinda ya jefa dubban matafiya cikin dawuwa.

Kamfanin na Arik shi ne, mafi girma da yawan jirage a Yammaci da Tsakiyar Afrika, kuma shi ne na uku da ya dakatar da aiki tun lokacin da matsalar tattalin arziki ta tsananta a Najeriya bayan Aero Contactor da First Nation.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.