Jirgin First Nation ya dakatar da aiki
Hukumar Kula da sufurin jiragen sama a Najeriya ta sanar da dakatar da ayyukan kamfanin jiragen saman First Nation kwana guda bayan kamfanin Aero Contractors ya dakatar da aikinsa.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar Mukhtar Usman ya ce dakatarwar ta biyo bayan bukatar sauya injin din daya daga cikin jiragen kamfanin da kuma bukatar sake duba lafiyar jiragen.
Jami’in ya ce babu yadda za su bar kamfanin ya ci gaba da aiki da jirgin guda
Mista Usman ya ce saboda irin wannan dalili ne aka sa kamfanin Aero ya dakatar da ayyukansa.
Sai dai kamfanin Aero wanda ya dakatar da aiki a ranar Alhamis ya danganta dalilin da yanayin tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu.
Dakatar da ayyukan Kamfanonin biyu na dada haifar da rashin ayyukan yi a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu