Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dattijai za ta saurari bahasi kan kasafin kudin 2017

Majalissar Dattejan Najeriya za ta saurare ra’ayi jama’a gobe litinni kan kasafin kudin shekarar 2017, na naira Triliyan sama da 7 da shugaba Buhari ya gabatar gabanta.

Shugaba Buhari a lokacin gabatarwa Majalisar dokokin kasar kasafin kudin 2017
Shugaba Buhari a lokacin gabatarwa Majalisar dokokin kasar kasafin kudin 2017 REUTERS/Stringer
Talla

Batun da ake bayanawa a matsayin irinsa na farko da majalisar ke shirin gudanarwa, a cewar kakkakin Majalisar, Aliyu Abdullahi, an dau wannan mataki ne domin bai wa masu ruwa da tsaki da sauran al’umma daman tofa albarkacin bakinsu kan kasafin kudin.

‘’Jin bahasin kan kasafin kudin shekarar 2017, shine zai bai wa Majalisar daman amincewa da ita’’, a cewar Aliyu Abdullahi.

Tun a shekarar da ta gabata shugaba Buhari ya gabatarwa Majalisa Kasafin da ya haura kasafin 2016.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.