Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Sarki Sunusi na shirin hana marasa karfi auren mace sama da guda

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II, ya ce kwamitin malamai na majalisarsa zai kafa wata doka da za ta hana marasa karfi auren mace fiye da guda daya.

Sarkin kano Mohammad Sunusi na Biyu
Sarkin kano Mohammad Sunusi na Biyu REUTERS/Stringer
Talla

Sarki Sunusi ya ce yin aure fiye da guda ga marasa karfi ganin basu da halin rike iyalin ya sabawa shari’ar Islama ga kuma matsalar da hakan ke haifarwa a sha’anin ilimi da kuma tarbiyar yara

Sarkin ya fadi hakan ne a yayin wani taro da ya halarta a Abuja babban birnin kasar.

Sarki Sunusi, ya ce zai tabbatar da cewa dokar ta bi dukkanin hanyoyin da suka dace domin gwamnatin jihar ta Kano ta tabbatar da ita.

Tun a shekarar da ta gabata Sarkin ya kafa kwamitin malaman don yin nazari tare da tsara yadda dokar zai kasance kafin gabatar da ita a gaban majalisar dokokin jihar.

Sai dai kuma wasu na ganin auren mata fiye da daya da mazan marasa karfi ke yi a jihar yana taimakawa wajen rage yawan mata da zawarawa da ke zaune ba miji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.