Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Najeriya ya kara tsawaita hutunsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai cigaba da kasancewa a birnin London inda ya je domin duba lafiyarsa na tsawon lokaci, bisa shawarar da likitocinsa suka bada.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari nbcnews
Talla

Mai bai wa shugaban Najeriyar shawara kan kafafen yada labarai Femi Adesina ya sanar da halin da ake ciki, bayan samun takardar da ke tabbatar da hakan daga shugaba Buhari da ke London.

Cikin takardar sanarwar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa ‘yan kasar dake yi masa addu’oi a Masallatai da mujami’u dan ganin ya samu lafiya.

Tun a ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata Buhari ya tafi birnin London don a duba lafiyarsa, inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ke rike da mukamin mukaddashin shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.