Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram-Taron Oslo zai tallafawa Tafkin Chadi da $672 mn

Taron kasashen duniya 14 da ke gudana a birnin Oslo na kasar Norway ya yi alkawarin samar da dalar Amurka miliyan 672 don tallafawa  miliyoyin mutane da rikicin Boko Haram ya shafa a tafkin Tchadi.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu. today.ng
Talla

Tuni dai kasashen suka soma tara kudin inda suka kuma yi alkawarin bada taimakon a  cikin shekaru uku, domin tallafawa mutane sama da miliyan 10 da ke cikin bukatar gaggawa a yankin tafkin Chadi.

Taron na da burin tara dala biliyan daya da rabi domin ayyukan jinkai a shekarar 2017 da muke ciki, a baki dayan kasashen da ke yankin tafkin Chadi.

Manyan Jami’an da ke halartar taron na Oslo a kasar Norway, sun hadar da ministoci daga kasashen Jamus, Najeriya, Nijar, Chadi, da Kamaru, sai kuma babban jami’in lura da ‘yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya Fillippo Grandi, da shugaban asusun  samar da Abinci na duniya Ertharian Cousin.

Yayin ganawar sa da kungiyoyin kishin al’umma ministan harkokin kasashen waje na Norway Borge Brende, ya ce duniya na neman mantawa da batun wadanda rikicin na Boko Haram ya shafa.

Halin yanzu  jama’a da dama na cikin mawuyacin hali a Najeriya da kuma yankin tafkin Chadi, sakamakon rikicin Boko Haram.

Rahotanni sun ce a yankin arewa maso gabashin Najeriya akwai mutane sama da miliyan 5 da ke fuskantar karancin abinci, sannan yara sama da dubu dari biyar na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Babban jami’in ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel Toby Lanzer, ya yi kira ga kasashen duniya da su waiwayi yankin cikin gagawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.