Isa ga babban shafi
Boko Haram

Tarayyar Turai za ta tallafawa Dakarun tafkin Chadi

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana aniyarta na tallafawa rundunar dakarun hadakar kasashen yankin tafkin Tchadi da kudin da ya kai Yuro Miliyan 50, domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Dakarun kasashen tafkin Chadi da ke fada da Boko Haram
Dakarun kasashen tafkin Chadi da ke fada da Boko Haram REUTERS/Stringer
Talla

An kafa rundunar ne a watan Mayu don yakar kungiyar Boko Haram da ke ikrarin yakin jihadin islama a Tarayyar Nijeriya da kuma ta fadada ayyukanta zuwa kasashe makwabta.

A ranar Litanin da ta gabata ne aka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a birnin Addis-Abeba na kasar Habasha.

Wadannan kudade kuma za su bada damar ginawa tare da kula da gyaran hedikwatar rundunar da ke birnin N’Djamena na kasar Chadi da kuma sauran rassanta da ke kasashen Cameroun da jamhuriyar Nijar.

Rundunar ta kunshi dakaru sama da 8000 na kasashen yankin tafkin Chadi da ta hada kasashen Kamaru da Nijar da Najeriya da Chadi da kuma Jamhuriyar Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.