Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi magana da Adeshina

Mashawarci na musamman ga shugaban Najeriya Femi Adesina ya ce sun zanta ta wayar tarho da shugaba Muhammadu Buhari da misalin karfe 2 da mintuna 3 agogon kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Talla

Cikin wani salo na nuna shauki bisa kiran da shugaban kasar ya yi masa, Femi Adesina ya ce shugaba Buhari ya kira shi ya jinjina masa bisa yadda ya ke kokarin kare kimar gwamnatin sa.

Ya ce shugaban ya kuma sanar da shi cewar har yanzu yana kan hutun sa a birnin Landon na Birtaniya, inda ya fada masa cewar yana fatan zai kara kiran sa a wani lokaci na gaba.

Femi Adesina ya bayyana farin cikin sa, bisa zantawar da ya yi da shugaban na Najeriya  kasancewar tsawon lokacin da Buharin baya kasar, Femi bai taba magana da shugaban kasar kai tsaye ba.

Shugaba Buhari ya soma daukar hutun kwanaki goma don zuwa Landan sai dai daga baya ya kara wasu kwanaki inda ya ce ya yi hakan ne bisa shawarar likitoci don tabbatar da koshin lafiyarsa kafin ya dawo Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.