Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya za ta kai karar NNPC a gaban EFCC

Kwamitin Majalisar Walikan Najeriya da ke nazari kan farashin albarkatun man fetir ya yi barazanar shigar da karar jami’an kamfanin mai na NNPC a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC sakamakon zargin su da hannu a wata badakalar kudaden ketare.

Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya ya yi barazanar shigar da karar ma'aikatan kamfanin mai na NNPC a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC saboda wata badakalar kudaden ketare
Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya ya yi barazanar shigar da karar ma'aikatan kamfanin mai na NNPC a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC saboda wata badakalar kudaden ketare AFP
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da wasu kamfanonin mai suka musanta karban kudaden duk da cewa babban bankin kasar CBN ya ce sun karba kudaden don gudanar da aikin mai a kasar.

Shugaban Kwamitin Raphael Nnanna Igbokwe ya ce, za su yi bincike mai zurfi don gano yadda badakalar ta rufa-rufa ta shafi jami’an NNPC.

A makon jiya ne hukumar EFCC ta cafke wasu darektocin CBN saboda zargin su da hannu a badakalar bada kudaden na ketare.

Tuni dai kwamitin ya bukaci karamin Ministan Mai na Najeriya Dr, Ibe Kachikwu da Gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele da su bayyana a gabansa a ranar Jumma’a mai zuwa don bada cikakkun bayanai kan wannan lamari mai sarkakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.