Isa ga babban shafi
Najeriya

Muna goyon bayan hukunta mai laifi- Miyetti Allah

Kungiyar Makiyayya ta Miyetti Allah da ke wakiltar Fulani a Najeriya ta bayyana cewa, tana goyon bayan hukunta duk wani mai laifi da ya karya doka a kasar.

Fulanin da ake zargi da sace Olu Falae rike da wani kaso daga cikin kudin fansar da suka karba
Fulanin da ake zargi da sace Olu Falae rike da wani kaso daga cikin kudin fansar da suka karba vanguardngr.com
Talla

Wannan na zuwa ne bayan wata babbar Kotun Tarayya da ke jihar Ondo a kudancin kasar ta yanke wa wasu Fulani bakwai hukuncin daurin rai-da-rai saboda da samun su da laifin sace tsohon Sakataren Gwamnatin kasar, Olu Falae.

A zantawarsa da RFI Hausa, shugaban kungiyar Miyati Allah ta kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardo ya bayyana cewa, suna goyon bayan hukunta masu laifi kamar yadda doka ta tanada, amma ya ce ba za su amince da hukumta wanda bai san hawa da sauka ba.

00:55

Muryar Ardo kan hukunta Fulani makiyaya

A ranar 21 ga watan Satumban 2015 ne aka yi garkuwa da Falae a yayin bikin cikarsa shekaru 77 da haihuwa.

Amma an sake shi bayan biyan Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Abubakar Auta da Bello Jannu da Umaru Ibarahim da Masa’ud Muhammad da Idris Lawal, da Abdulkadir Umar da kuma Babawo Kato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.