Sabbin dabarun hana satar shanu a Najeriya
A kokarin samar da mafita a kan matsalar satar shanu da kuma rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma, wanda ke sanya wasu kwararru fannin kimiyya samar da wata na’ura ta hanyar yin allura ga dabbobi don sanin asalin mai su.
Wallafawa ranar:
Kwararru a fannin kimiyya sun tabbatar da cewa yin amfani da wannan fasahar zamani a kan dabbobi za ta taimaka wajen dakile satar shanu da ya zama ruwan dare a Najeriya wanda hakan ke kawo koma baya ga fannin tattalin arziki da kuma na tsaro a kasar .
Bikin gwajin na’urar da aka gudanar a garin Kaduna ya samu halartar dukkanin masu ruwa da tsaki daga bangarorin Fulani makiyaya, jami’an tsaro da kwararru a fannin kiwon lafiyar dabbobi da kuma a fannin sadarwa.
Wakilinmu na Kaduna Aminu sani sado na dauke da Karin bayani.
Sabbin dabarun hana satar shanu a Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu