Isa ga babban shafi

Al'ummar Allawa da ke jihar Neja na tserewa daga garin bayan janye sojoji

Jami’an rundunar sojojin Najeriya sun janye daga sansaninsu da ke kauyen Allawa na karamar hukumar Shiroro da ke Jahar Neja, lamarin da ya sanya al'ummar garin tserewa daga gidajensu.

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. © AFP
Talla

Janyewar da sojojin suka yi daga kauyen na Allawa da ke cikin yankunan da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, ya sanya mazauna garin musamman mata da tsofaffi da kuma kananan yara yin tattaki na kimanin kilomita 50 a kafa don cira da rayuwarsu.

Wasu daga cikin mazauna garin da suka zanta da jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya, sun bayyana cewar a Alhamis din nan ne suka ga sojojin na kwance tantunansu, lamarin da ya tada hankalin al’ummar garin.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce janyewar sojojin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da daya daga cikin motocinsu ta taka nakiya a kan hanyar Allawa zuwa Pandogari, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da kuma raunata wasu da a yanzu ke samun kulawa a asibiti.

Wannan lamari dai na zuwa ne mako guda bayan da sojoji 6 da ‘yan sakai suka rasa rayukansu, a wani harin kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yi musu a Roro.

Wani mazaunin garin na Allawa Malam Yahuza, ya ce tun da misalin karfe 4 na asubahi mutanen garin suka fara barin gidajensu don neman mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.