Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kona gonakin abinci a jihar Neja

Wasu ‘yan bindiga sun kona gonaki 20 na masara da waken suya da dawa  a wajen garin Kontagora a can Karamar Hukumar Kontagora ta jihar Neja a Najeriya.

'Yan bindiga sun addabi wasu jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu jihohin Najeriya. © dailypost
Talla

Daya daga cikin manoman da aka gona gonakinsu, ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kuma ajiye musu wata wasikar gargadi, inda suka bukaci kowanne manomi ya biya su naira miliyan 30 ko kuma su fuskanci farmaki.

‘Yan bindigar sun ajiye lambar wayar da za a kira su, kuma tuni wasu daga cikin manoman suka tuntube su, inda suka shaida musu cewa, lallai su ne suka kona musu gonaki, sannan suka yi musu barazanar daukar mataki a kasnu matsawar suka gaza biyan kudin da aka sanya musu.

Yanzu haka wadannan manoma na rokon gwamnatin tarayya da ta jihar da su kawo musu agajin magance wannan matsalar ta kaddamar da hare-hare kan manoma.

‘Yan bindigar sun kona albarkatun gonar ne da suka isa girbi  kamar yadda manoman suka bayyana, suna masu cewa, suna kan shirye-shiryen kawo abincin da suka noma gidajensu ne don ciyar da iyali amma hakan bai yiwuwa saboda harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.