Isa ga babban shafi
Najeriya

Sarkin Kano ya yi barazanar rusa gidan Kadiriyya

A Najeriya Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi barazanar rusa shalkwatar Darikar Kadriyya ta Afrika ta Yamma da ke birnin, muddin ‘ya'yan tsohon shugaban Darikar marigayi Sheikh Nasiru Kabara suka gaza wajen hada kawunansu.

Mai Martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi
Mai Martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi
Talla

Muhammadu Sanusi na biyu ya yi wannan barazana ce lokacin da daya daga cikin 'ya'yan marigayin Nasiru Kabara, Sheikh Askiya Nasiru Kabara ya ziyarce shi a fadarsa.

Tun bayan nada sabon shugaban Darikar Kariballa Nasiru Kabara ake ci gaba da samun sa-in sa tsakaninsa da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Sarkin na Kano ya kuma bayyana takaicinsa ganin yadda ‘yayan na Nasiru Kabara suke rikici da juna, in da ya bayyana cewa kowanne daga cikinsu na iya wakiltar mahaifin nasu a maimakon takun saka da juna.

00:45

Muryar Sarkin Kano kan rusa gidan Kadiriyya

Mai martaba Sunusi na biyu ya kuma jinjina wa Malam Nasiru Kabara kan yadda ya ke jaorantar mutane kimanin miliyan 1 a bikin hawan maukibi a lokacin rayuwarsa ba tare da samun tashin hankali ba.

Sannan ya kara da cewa daukan matakin rusa gidan marigayin don gina masallaci ya fi alheri fiye da  yadda 'ya'yansa ke kokarin wargaza abin da ya bari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.