Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta nemi hadin kan Sarakuna
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce har yanzu tana dakon amincewar shugaban kasar Muhd Buhari, kan bukatar da ta gabatar masa, dangane da daukar sabbin jami’an ‘yan sanda 30,000 duk shekara har tsawon shekaru 5.
Wallafawa ranar:
Maigari Abbas Dikko, mataimakin babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da samarwa da kuma kayan aikin rundunar ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu.
Dikko ya bukaci hadin sarakunan gargajiya da gwamnoni wajen tantance sabbin jami’an ‘yan sandan da za’a dauka da zarar shugaba Buhari ya amince da bukatar.
A cewar mataimakin sifeto janar Dikko, a halin da ake ciki, yawan jami’an ‘yan sandan Najeriya bai zarta 380,000 ba, lamarin da ya sa tilas a dauki karin 155,000 cikin shekaru biyar. domin cika ka’idar da majalisar dinkin duniya ta ware kan aikin dan sanda.
Karkashin ka'idar dai kamata yayi duk jami'in dan sanda guda ya kula da mutane akalla 400.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu