Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

'Yan Najeriya miliyan 57 basa samun ruwan sha mai tsafta

Wallafawa ranar:

Wani Bincike ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 57 basa samun tsaftacaccen ruwan sha, yayin da wasu ‘yan kasar miliyan 130 kuma ke bayan gida a fili. Kungiyar WaterAid ta bayyana haka, yayin gudanar da a bikin ranar kasa ta duniya da akeyi yau Litinin, wanda ke nazari kan halin da duniya ke ciki dangane da tsafta. Kungiyar tace wannan na daga cikin matsalar dake haifar da cututtuka a tsakanin al’umma, wadanda ke sanadiyar mutuwar yara kanana 45,000 kowacce shekara. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Usman Sule Riruwai, kwamishinan ruwa na Jihar Kano, kan wannan matsala da ke fuskantar Najeriya.

WaterAid Nigeria - Ending poverty starts with water [nid:500612160]
WaterAid Nigeria - Ending poverty starts with water [nid:500612160] wateraid.org/ng
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.