Isa ga babban shafi
Najeriya

An gurfanar da Sule Lamido a gaban Kotu

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Shiya ta daya da ke Jihar Kano ta gurfanar da Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamdido a gaban wata kotu da ke Garin Dutse.

An gurfanar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido a gaban kotu
An gurfanar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido a gaban kotu
Talla

Ana dai tuhumar Lamido ne da laifuka hudu, da suka hadar da ingiza Jama'a, da bata sunan gwamna Mai ci, sai kuma barazana ga zaman lafiya.

Sai dai an dage sauraron shara'ar zuwa ranar Alhamis ba tare da bayar da Belin tsohon gwamnan kamar yadda lauyoyinsa suka bukata ba.

Alkali Muhammad Lamin ya kuma bada umarni ci gaba da tsare Lamido a gidan yari har zuwa lokacin ganin yiwuwar bayar da belinsa.

Tsohon gwamnan dai ya musanta tuhume-tuhume da ake masa.

Jam'iyyar PDP a Jihar Jigawa na zargin cewar ana yiwa Tsohon Gwamnan bita da kullin siyasa ne.

Wakilinmu Abubakar Dandago da ya halarci zaman Kotun, ya rawaito cewa, Zanga-zanga ta barke a haraban Kotun tsakanin daruruwan magoya bayan Lamido, abin da ya tursasa jami'an tsaro amfani da hayaki mai sa kwala don tarwatsa cuncurundo jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.