Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekarau ya bai wa ‘yansanda kwanaki 14 su wanke shi

Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bai wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan kasar kwanaki 14 dan wanke shi daga zargin takardar da suka ce tana alakanta shi da kashe Sheikh Jaafar Adam ko kuma su gurfana a gaban kotu.

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau
Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau THISDAY
Talla

A wata wasika da ya sanyawa hannu, Malam Shekarau ya bukaci Sufeto Janar din ya fito fili ya yiwa ‘Yan Najeriya bayani kan abinda takardar da ake zargi ta kun sa.

Da Kuma banbanta binciken da ‘Yan Sandan suka yi a karkashin Hafiz Ringim wanda Emmanuel Ojukwu ya shaidawa duniya.

Shekarau ya ce yin Karin haske kan takardar na da matukar tasiri a gare shi da daukacin magoya bayan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.