Isa ga babban shafi
Najeriya

Mukaddashin shugaban Najeriya ya gana da Sarakuna

Mukaddashin Shugaban Kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Sarakunan yankin arewacin kasar, a yunkurinsa na samar da hadin-kai bayan rashin jituwar da ta kunno kai, sakamakon wa’adin da kungiyoyin matasan arewacin suka bai wa ‘yan kabilar Igbo, na su fice daga yankin nasu kafin ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Saa’d, tare da mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo and da kuma mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Janar Babagana Mongunu yayin taro da Sarakuna a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Saa’d, tare da mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo and da kuma mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Janar Babagana Mongunu yayin taro da Sarakuna a fadar gwamnati da ke Abuja. NAN
Talla

Matakin matasan arewacin, yana a matsayin martini ga zanga-zangar da Igbon ke gudanarwa na neman kafa kasar Biafra.

Jim kadan bayan ganawar su da mukaddashin shugaban kasar, daya daga cikin Sarakunan da suka halarci taron, Etsu Nupe, wato Sarkin Bida, Alhaji Yahaya Abubakar, ya shaidawa wakilinmu Muhammadu Kabiru Yusuf cewa, taron ya cimma matsayar bai wa Sarakunan gargajiya cikakkiyar damar amfani da hikimarsu wajen warware takkadamar da ta taso cikin lumana.

Dan haka a cewars mai martaba Sarkin na Bida zancen ballewar wani sashin kasar nan ma babu shi.

01:00

Sarkin Bida

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.