Isa ga babban shafi
Najeriya

Borno: Matsalar safarar miyagun kwayoyi ta yi kamari

A daidai lokacin da ake tunawa da ranar yaki da sha ko tu’ammali da miyagun kwayoyi a duniya, rahotanni daga jihar Borno, na cewa lamarin ya kazanta a jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Matsalar safarar miyagun kwayoyi na kokarin zama barazana a Borno
Matsalar safarar miyagun kwayoyi na kokarin zama barazana a Borno togoqueens.com
Talla

A lokuta da dama jami’an tsaro, sun sha kama miyagun kwayoyi da ake shirin safararsu musamman daga Maiduguri zuwa yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Garba Muhd Bala, shi ne shugaban hukumar NDLEA mai kula da shiyyar Gamboru Ngala, ya kuma shaidawa RFI Hausa cewa, babban kalubalen da ke gaban hukumar shi ne rashin samun hadin kan al’ummar yankunan da matsalar tsaron ta shafa, wajen yakar tu’ammuli da miyagun kwayoyin.

A cewar Bala, akwai zargin cewa masu safarar miyagun kwayoyin suna cinikayya ne da mayakan Boko Haram, idan aka yi la’akari da cewa, mafi akasarin jama’ar da matsalar tsaron ta shafa suna kokarin ganin yadda zasu inganta rayuwarsu ce.

00:40

Borno: Matsalar safarar miyagun kwayoyi ta yi kamari NDLEA-GARBA-MUHD-BALA

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.