Tsohon Minista a Najeriya ya lashe kyautar yabo ta Duniya
Shugaban bankin raya kasashen Afirka ADB ko kuma BAD, Akinwumi Adesina, ya lashe kyautar yabo ta duniya da ake bai wa wanda ya fi nuna kwazo wajen bunkasa aikin gona da Gidauniyar bada kyautar yabo kan ayyukan gona WFP ke bayarwa a kowace shekara.
Wallafawa ranar:
Shugaban Gidauniyar Kenneth Quinn, wanda ya sanar da haka a birnin Washington, ya ce Adesina, tsohon ministan ayyukan gona a Najeriya, ya taka gagarumar rawa wajen shinfida tsarin aikin gona mai karko kuma wanda zai taimaka wajen yaki da yunwa musamman a Afirka.
Sakamakon wannan nasarar Adesina zai karbi kyautar kudi dala 250,000.
Alhaji Muhammad Magaji, shi ne sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya, yayin zantawar da yayi RFI Hausa, idan aka yi la’akari da gudunmawar da ya bada wajen tallafawa kananan manoma a Najeriya, a lokacin da yake ministan ayyukan gona, lashe kyautar ba abin mamaki bane.
Muhammad Magaji
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu