Rage makin shiga manyan makarantu ya janyo cece-kuce a Najeriya
A Najeriya, masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun fara tofa albarkacin bakin su bayan da hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a kasar ta sanar da kayyade makin da dalibai ke bukata kafin samun gurbin karatu a jami’o’I da sauran manyan makarantu. Hukumar wadda ake kira da Jamb a takaice, ta ce kowanne dalibi na bukatar maki 120 kafin samun gurbin karatu a jami’a ko kuma maki 100 domin shiga kwalejojin kasar. Wakilinmu na Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya yi nazari kan wannan batu ga kuma rahoton daya aiko mana.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rage makin shiga manyan makarantu ya janyo cece-kuce a Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu