Isa ga babban shafi
Najeriya

Tilas duk wani mai korafi ya bi tsarin doka - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin tabbatar da dunkulewar kasar a karkashin gwamnatinsa, inda ya dora alhakin bullar kungiyar IPOB mai ikirarin neman ballewa daga kasar kan wuce gona da iri da wasu ke yi, dalilin ‘yancin fadin albarkacin baki da gudanar da siyasa da gwamnatinsa ta bai wa al’ummar kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne cikin sakonsa ga 'yan kasar na bikin cikar Najeriya shekaru 57 da samun ‘yancin kai.

Shugaban Najeriyar, ya kuma nuna bacin ransa, kan yadda ya ce dattawan yankin kudu maso gabashin kasar, suka gaza tsawatarwa matasan da ke ikirarin neman ballewa daga kasar, duk da cewa sun shaida yadda makamancin wannan yunkuri a shekarar 1967 ya haddasa hasarar rayuka sama da miliyan biyu.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa, duk wani yunkuri na fasalta kasa ko sauya kundin tsarin mulki, dole ne ya bi hanyoyin da suka dace, ta hanyar mika lamarin ga majalisun dokokin Najeriya.

Dangane da yankin Niger Delta kuwa, Buhari ya ce zasu cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, wajen maido da cikakken zaman lafiya a yankin, tare da share jerin koken da suka gabatarwa gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.