Isa ga babban shafi
Najeriya

Wasu ‘Yan Biafra sun yi ikirarin kafa gwamnati

Shugaban wata kungiya a kudancin Najeriya da ake kira Biafra Zionist Federation Benjamin Onwuka ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Biafra na riko, tare da zayyana sunayen ministocin sabuwar gwamnatinsa.

Tutar kasar Biafra da wasu 'yan kabilar Igbo ke fafutikar tabbatarwa a kudancin Najeriya
Tutar kasar Biafra da wasu 'yan kabilar Igbo ke fafutikar tabbatarwa a kudancin Najeriya STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

A yayin da ya ke sanar da matakin a Enugu, Onwuka ya zana sunan Farfesa Chukwuma Solodu a matsayin Gwamnan Babban Banki da Farfesa Pat Utomi a matsayin ministan harkokin waje, da Farfesa Jerry Gana a matsayin ministan sufuri sai Labaran Maku a matsayin ministan sufurin sama da kuma Oruma Oteh a matsayin Ministan kudi.

Akwai Benny Lar da aka nada sakataren gwamnati tare da nada wasu a matsayin jekadun Biafra a Amurka da wasu manyan kasashen duniya.

Mista Onwuka ya ce gwamnatin rikon kwaryar za ta yi aiki ne nan da wata daya daga ranar 1 ga Agusta.

Sannan a cikin sanarwar ya ce Isra’ila ce za ta samar da tsaro a Biafra yayin da kuma kamfanonin Amurka za su tafiyar da harakar arzikin mai a yankin.

Sai dai matakin ya yi karo da kungiyar da ke fafutikar kafa kasar Biafra ta IPOB inda ta zargi Onwuka da yin zagon kasa ga gwagwarmayar da suke ta tabbatar da kasar Biafra.

Fafutikar kafa kasar Biafra ya taba jefa Najeriya cikin yakin basasa a 1967 zuwa 1970 al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan Miliyan daya.

Wasu Kungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun bukaci Gwamnatin kasar ta gaggauta daukar mataki kan ‘Yan Biafra da suka sanar da kafa Gwamnati.

Jagoran kungiyar matasan na kano Kwamared Kabir Saidu Dakata ya shaidawa RFI Hausa cewa dokar Najeriya ta yi tanadi akan duk wani tsagera ko wata kungiya da ta ce za ta ware kanta daga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.