Isa ga babban shafi
Najeriya

An fara shari'ar 'yan Boko Haram sama da dubu 2 a Najeriya

A Najeriya, a wannan Litinin za a fara shari’ar akalla mutane dubu 2 da 300 da ake zargin cewa magoya bayan kungiyar Boko Haram ne da yanzu haka ke tsare a hannun jami’an tsaron kasar.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram a Najeriya
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram a Najeriya pmnewsnigeria
Talla

Za a fara shari’ar ne a asirce da mutane 1,670 wadanda ake tsare da su a wani barikin soji da ke Kainji a cikin jihar Niger, yayin da wani lokaci a gaba za a yi shari’ar kashi na biyu na ‘yan kungiyar ta Boko Haram 651 da ke tsare a barikin Giwa da ke birnin Maiduguri a jihar Borno kamar dai yadda bayanai suka nuna.

Gabanin wannan lokaci, mutane 13 ne kadai aka gurfanar a gaban kotu bisa zargin alakarsu da Boko Haram, in da kuma aka samu mutane tara daga cikinsu da hannu a rikicin kungiyar.

Tun lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari shekaru takwas da suka gabata, ake tsare da mutanen da ake zargi a tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 20 musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.