Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi bikin samun ‘yancin kai tare da Sojojin Najeriya a Maiduguri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bikin cika shekaru 57 da samun ‘yancin kan Najeriya tare da rundunar Lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram a garin Maiduguri na Jihar Borno.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da rundunar Lafiya Dole da ke yakar Boko Haram a Borno
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da rundunar Lafiya Dole da ke yakar Boko Haram a Borno RFIhausa/Bilyaminu
Talla

Shugaban ya kai ziyarar ne a yankin arewa maso gabashin kasar domin duba irin ayyukan da dakarun sojin kasar ke yi da kuma duba halin da 'yan gudun hijira ke ciki.

A jawabinsa ga ‘Yan kasa Shugaba Buhari ya yi mummunar suka kan masu neman raba kasar bayan yakin basasar da ya hallaka mutane sama da miliyan 2 a shekarar 1967.

Buhari ya ce abin takaici ne yadda wasu matasa wadanda ba a Haifa ba a shekarar 1967 ke neman jefa kasar cikin wani sabon tashin hankali.

Shugaban ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda shugabannin wannan yanki suka zuba ido suna kallonsu, inda ya ke cewa Najeriya ba za ta rabe a karkahsin mulkinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.