Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya amince da kwangilar Naira biliyan 640 a London-Baru

Shugaban Kamfanin mai na Najeriya NNPC, Maikanti Baru ya bayyana cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bai wa kamfanin umarnin bayar da kwangilar harkar mai ta Naira biliyan 640 a lokacin da ya ke jinya a birnin London kamar yadda jaridar Premiumtimes da ake wallafa a kasar ta rawaito.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Mr. Baru ya ce, akalla shugaba Buhari ya amince da kwangiloli guda biyu daban-daban a ranakun 10 da 31 na watan Julin da ya gabata da kudinsu ya kai Dala biliyan 1 da miliyan 780.

Baru ya ce, Buhari ya bada da kwangilar ce a lokacin jinyarsa a London da kuma bayan ya mika rgamar tafiyar da mulkin kasar ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Duk da dai Buhari ya mika ragamar tafiyar da kasar ga Osinbajo bayan neman izini daga Majalisar Dattijai, amma ya ci gaba da nuna karfin ikonsa a yayin jinyar a London ta hanyar bada umarnin kwangilar kamar yadda Premiumtimes ta ambata a shafinta na intanet.

Wannan dai na zuwa ne bayan tankiyar da aka samu tsakanin Baru da karamin Ministan mai, Ibe Kachikwu, wanda ya zargi Baru da yin gaban kansa wajen tafiyar da harkokin NNPC ba tare da tuntubar sa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.