Najeriya
Kada ku kai hari yanzu - Clark
Shugabannin da suka fito daga yankin Naija-Delta da ke Najeriya sun bukaci matasan yankin masu tayar da 'kayar baya da su janye barazanar da suka yi na kaddamar da kai hare hare kan bututun mai.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaban 'kungiyar dattawan yankin Edwind Clark ya bukaci matasan da su kai zuciya nesa, domin baiwa gwamnati damar aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla mai dauke da kudirori 16.
A karshen mako kungiyar Naija Delta Avengers ta yi barazanar za ta fara kai sabbin hare-hare saboda abinda ta kira rashin cika alkawarin gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu