Babu rabuwa tsakanin kabilar Ibo da Najeriya - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci al’ummar kasar na yankin kudu maso gabashi, su yi watsi da farfagandar ‘yan neman tada zaune tsaye, masu neman ballewa daga kasar.
Wallafawa ranar:
Buhari yayi kiran ne, a garin Abakaliki, a lokacin jawabi ga taron jama’ar garin, yayinda ya ziyarci jihar Ebonyi a ranar Talata.
Shugaban babu rabuwa tsakanin kabilar Ibo da Najeriya, kan haka ne kuma ya ziyarce su, don tabbatar zaman Najeriya a dunkule. Zalika ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnatinsa zata cika alkawuran da ta dauka na aiwatar da manyan ayyuka a yankin.
A lokacin ziyarar ce kuma sarakunan gargajiya na Kabilar Ibo, a karkashin jagorancin Eze Eberechi Dick, suka karrama Buhari, da mukamin sarautar gargajiya ta Ochioha Ndigbo wato (jagora ga ‘yan kabilar Ibo).
A baya wani bangare na kabilar ta Ibo, ya sha kokawa da nuna adawa ga gwamnatin Muhammadu Buhari, bisa zargin baya damawa da ‘yan kabilar cikin harkokin kasa, lamarin da ya kai ga kungiyar IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu karfafa aniyar da ta dade da kudurewa ta ballewa daga Najeriya. Sai dai an kwantar da tashin hankalin da nemi barkewa, bayan matakan da hukumomin tsaron kasar suka dauka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu