Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 18 sun mutu a harin Maiduguri

Akalla mutane 18 sun rasa rayukansu yayin da 29 suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan kunar bakin wake suka kaddamar a yamamacin jiya a birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya.

Kungiyar Boko Haram ta sha kai farmaki a Muna Garage da ke jihar Borno a Najeriya
Kungiyar Boko Haram ta sha kai farmaki a Muna Garage da ke jihar Borno a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

An ji karar fashe-fashen bama-bamai a birnin na Maiduguri a yayin da mayakan da ke zargin ‘yan Boko Haram ne ke tayar da bama-baman a Muna Garage da ke karamar hukumar Konduga.

Wakilin sashen hausa na rfi, Bilyaminu Yusuf ya tabbatar ma na cewa, mata biyu da maza biyu ne suka kai farmakin kuma daya daga cikin matan ta tayar da bam din da ke jikinta a wani masallaci a dai dai lokacin da jama’a ke sallar Magariba.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Borno, Victor Isuku ya ce, ana zaton mayakan Boko Haram ne suka kaddamar da farmakin.

Ba a karon farko kenan ba da ‘yan Boko Haram ke kai farmaki a Muna Garge mai cike da hada-hadar jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.