Isa ga babban shafi
Najeriya

Yara dubu 270 sun kamu da HIV a Najeriya

Asusun bunkasa ilimin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana cewa, kimanin kananan yara dubu 270 ne ke dauke da cutar Sida ko kuma HIV a Najeriya a bara.

Da dama daga cikin kananan yara na rasa maganin rage kaifin cutar HIV a Najeriya
Da dama daga cikin kananan yara na rasa maganin rage kaifin cutar HIV a Najeriya Reuters/Siphiwe Sibeko
Talla

Alkaluman na nuni da cewa, Najeriya na da 50 cikin 100 a kananan yara tsakanin shekaru 14 da ke fama da cutar a yankin yammaci da tsakiyar Afrika a shekarar 2016.

Kazalika an samu sabbin yara dubu 37 da suka kamu da cutar a Najeriya daga cikin jumullar dubu 60 a yankin yammaci da tsakiyar Afrika.

Majalisar Dinkiin Duniya ta yi gargadi game da tsaikon da ake samu wajen yaki da cutar a yankin yammaci da tsakiyar Afrika, yayin da akasarin masu dauke da cutar ke rasa maganin rage kaifinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.