Najeriya
An sake ceto daya daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok
Rundunar sojin Najeriya ta sake ceto daya daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a cikin watan Afrilun shekarar 2014.
Wallafawa ranar:
Talla
An ceto yarinyar ce mai suna Salomi Pogu, a garin Pulka da ke karamar hukumar Gwoza a jahar Borno.
Pogu ita daliba ta 86 a jerin sunayan ‘yan mata fiye da 200 da yanzu haka wasunsu ke ci gaba da kasancewa a karkashin mayakan Boko Haram. Wakilinmu Bilyaminu Yusuf yana dauke da rahoto a kai.
An sake ceto daya daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu