Isa ga babban shafi
Najeriya

Mun kama jami'an 'yan sanda mata a Maiduguri- Shekau

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon Bidiyo ta kafofin sadarwa na zamani, in da yayi ikirarin cewa a halin yanzu sun yi garkuwa da wasu jami'an 'yan sanda mata da suka kama a hanyar Maiduguri zuwa Damboa da ke jihar Borno na Najeriya.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da mayakansa
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da mayakansa AFP PHOTO/YOUTUBE
Talla

Sakon bidiyon na tsawon minti 16 ya nuna Abubakar Shekau ba a cikin karsashi ba sosai kuma bai faye motsa barin jikinsa ba, kamar yadda ya yi a hotunan bidiyon da ya fitar a can baya.

Shekau ya ce, jami'an 'yan sanda matan na hannunsu a matsayin bayi.

Shekau ya kuma bayyana malaman addinin Islama a Najeriya a matsayin masu ci da Al-Kur’ani, yayin da ya ce, malaman sun manta da mahaliccinsu.

Kazalika mayakan na Boko Haram sun kira kansu a matsayin musulmi na asali.

Shekau ya kuma bayyana sarakunan gargajiya na Najeriya a matsayin makaryata da ke yaudarar jama'arsu.

Shugaban na Boko Haram ya saba aike wa da sakwannin bidiyo, duk da cewa a can baya an ce an kashe shi.

07:09

Muryar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

A zamanin tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan dai, an bukaci sojin kasar da su kamo shi da ransa.

Masana harhada hotunan bidiyo na ganin wadannan hotuna da ya ke fitarwa na gaske ne, ba wai shiri aka yi ba, da wasu ke cewa ya dade da mutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.