Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Najeriya da na kasashen tafkin Tchadi sun kaddamar da babban harin kan Boko Haram

Sojojin tarayyar Najeriya dake samun taimako daga takwarorinsu na kasashen dake makwabtaka da su, sun kaddamar da wasu manyan hare hare kan bangarori biyu na mayakan Boko Haram da shuwagabaninsu biyu, a yankin arewa maso gabashin kasar, kamar yadda rundunar sojan Najeriya ta sanar.

Shugaban rundunonin sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai na cewa mayakan Boko Haram 700 suka mika wuya.
Shugaban rundunonin sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai na cewa mayakan Boko Haram 700 suka mika wuya. thenewsnigeria
Talla

Dakarun kasashen kamaru, Tchadi, Jamhuriyar Niger da kuma Tarayyar Nigeria ne, suka durfafi sansanonin da shuwagaban mayakan na Boko Haram, Abubakar Shekau, dake cikin dajin Sambisa, da Mamman Nur, dake yankin tafkin Tchadi, yankunan biyu dake jihar Borno a Nigeria, inda mayakan ke ci gaba da haifar da zaman zullumi a cikin jama’a.

A cewar rundunar sojan Nijeria, fadan baya bayan nan da aka gwabza ta yi nasarar kashe mayakan na Boko Haram da dama, tare da tilastawa wasu mika kansu ga sojoji.

Wani babban hafsan soja da bai ambaci sunasa ba a Abuja, ya ce Mamman Nur dake jagorantar reshen mayakan Boko Haram da suka balle suka koma kungiyar ISIS ya samu rauni a fadan, kuma daya daga cikin matansa ta rasa ranta, a barin wutar da jiragen saman yakin Najeriya suka yi a kansu a ya yin da shi kuma Abubakar Shekau shugaban na Boko Haram, a halin yanzu ya kasance tamkar gajiyayen dokin da ya gaji da gudu daga yanzu a kowane lokaci zai iya faduwa

A wata sanarwa kakakin rundunar sojan ta Najeriya janar Sani Usman Kuka sheka ya ce hare haren, sojan da ake kira "Deep Punch 2" ya cimma muhimman nasarori samu yawan gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.