Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta daure Kwamandan Boko Haram shekaru 60

Wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Kainji a jihar Niger ta daure kwamandan kungiyar Boko Haram shekaru 60 a gidan yari bayan ya amince da laifukan da aka tuhume shi da aikatawa.

Abba Umar, Boko Haram Commander in Nigeria sentenced to 60 years in prison
Abba Umar, Boko Haram Commander in Nigeria sentenced to 60 years in prison Daily Trust/Nigeria
Talla

Kotun ta bukaci tsare Abba Umar mai shekaru 22 a gidan kaso har lokacin tsufarsa bayan ya rasa dukkanin wani kuzari.

An cafke Umar ne bayan wani harin mota makare da bama-bamai da ya jagoranci kaddamarwa a makarantar sakandaren horar da matukan jirgin sama a jihar Gombe wato Gombe Secondary School Pilot a ranar 7 ga watan Julin shekarar 2014. Sai dai harin bai yi nasara ba.

Matashin bai nuna nadma kan laifukan da ya aikata ba, yayin da ya lashi takobin komawa dajin Sambisa da zaran an sake shi don ci gaba da kaddamar da hare-hare tare da mayakan Boko Haram.

Umar ya ce, akwai zaratan mayakan Boko Haram da ke karkashinsa kuma shi jagora ne a cikinsu.

Tuni masharhanta suka ce, rayuwar al’umma na cikin hadari da zaran Umar ya kammala wa’adin zaman gidan kaso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.