Isa ga babban shafi
Najeriya

Iyayen Dalibai Mata Na Cigiyar 'Ya'yan su Bayan Harin Boko Haram A Yobe

Rahotanni daga garin Dapciya dake jihar Yobe a Najeriya na cewa jami’an Gwamnatin jihar da iyayen makarantar mata dake garin na kididdigan dalibai mata da ba’a gansu ba tun yammacin littini da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai samame garin.Majiyoyin samun labarai na cewa dalibai da yawa sun bazama daji saboda firgici har wasu sun sami saran maciji.Alhaji Ardo Mohammed na daya daga cikin mutanen da har yammacin Talata bai ga ‘yar sa ba amma ya ga saura abokan 'yar sa.Wasu majiyoyi na cewa an sami tsauraran matakan tsaro bayan harin da aka kai yammacin Littini.Majiyoyi sun shaida mana cewa maciji ya sari wata 'yar Bautan kasa dake makarantar bayan da ta bazama cikin daji saboda tsoro a lokacin da 'yan kungiyar Boko Haram suka afka cikin makarantar matan.Akwai kuma wani mutun da akace ya sami karaya a lokacin da yake neman tserewa daga harin.

Sojan Najeriya bayan da suka fatattaki 'Yan Kungiyar Boko Haram daga jihar Yobe kwanan baya.
Sojan Najeriya bayan da suka fatattaki 'Yan Kungiyar Boko Haram daga jihar Yobe kwanan baya. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.