Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta sako mu ne saboda Musuluncinmu- 'Yar Dapchi

Daya daga cikin ‘yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram ta dawo da su gida bayan sace su, ta shaida wa RFI Hausa cewa mayakan sun sako su ne saboda kasancewarsu Musulmai, in da suka ci gaba da tsare daliba guda saboda kasancewarta Kirista.

A'isha Alhaji Deri, daya daga cikin 'yan matan da Boko Haram ta sako bayan sace su tun a ranar 19 ga watan Fabairun da ya gabata
A'isha Alhaji Deri, daya daga cikin 'yan matan da Boko Haram ta sako bayan sace su tun a ranar 19 ga watan Fabairun da ya gabata RFIhausa/Bilyaminu
Talla

A yayin zantawarta da Wakilinmu Bilyaminu Yusuf, Ai’sha Alahaji Deri ta ce, sun samu kulawar da ta dace daga hannun mayakan na Boko Haram

A’isha ta bayyana cewa, mayakan ba su ci zarafinsu ba ta hanyar lalata da su kamar yadda jama’a da dama ke fargaba bayan saceewar.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren cikakken rahoton kan sakin 'yan matan na Dapchi

03:06

Boko Haram ta sako mu ne saboda Musuluncinmu- 'Yar Dapchi

Dalibar ta kara da cewa, ‘yan mata biyar daga cikin su sun rasa rayukansu ne sakamakon wahalhalun zirga-zairgar mota bayan sacewar, amma ba Boko Haram bace ta kashe su da hannunta.

Yusuf ya jiyo mana cewa, mayakan na Boko Haram ne suka gudanar da jana’izar matan da suka rasu kamar yadda Musulunci ya tanada.

Tun dai a ranar 19 ga watan Fabairu ne mayakan suka sace ‘yan matan bayan sun dirar wa makarantarsu ta Dapchi da ke jihar Yobe a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.