Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Zamfara ya yi murabus daga mukamin shugaban jami'an tsaro

A Najeriya, Gwamnan Zamfara Abdulazizi Yari ya sanar da yin murabus daga mukamin shugaban jam’ian tsaron jihar, la’akari da yadda har yanzu jami’an tsaro suka kasa kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari.
Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari. TheCable
Talla

Yayin da ya ke shaidawa manema labarai matakin da ya dauka a jiya a Talata Mafara, gwamna Yari ya ce hakan ya zama tilas, domin bashi da ikon sarrafa jami’an tsaron da ke kokarin shawo kan hare-haren ‘yan bindiga da ake ci gaba da samu a jihar ta Zamfara.

A cewar sa abin takaici ne a ce gwamna bashi da ikon baiwa jami’an tsaro umarni a bi, akan abin da ya shafi, daukar matakai ko dabarun kare rayuka da dukiyar jama’a a jiharsa daga hare-haren ‘yan bindiga.

Jawabin gwamnan jihar ta Zamfara, ya zo ne kwanaki kalilan, bayan da ya ya bukaci majalisun tarayyar Najeriya su cire wa gwamnoni mukamin da aka lakaba musu na shugabannin jami’an tsaron jihohinsu.

Yari ya ce gwamnonin ba sa bukatar mukamin ne la’akari da cewa, basu da cikakken ikon sarrafa jami’an tsaron da ke jihohinsu, ta hanyar hukuntawa, kora ko kuma daukar sabbin jami’an tsaron, duk da cewa suna amsa mukamin shugabannin jami’an tsaron jihohin na su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.