Isa ga babban shafi
Najeriya

"Kisan Hauwa ba zai hana ceto wadanda ke hannun Boko Haram ba"

Gwamnatin Najeriya, sauran jama’a a ciki da wajen kasar, da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya, suna cigaba da nuna alhini dangane da kisan da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi wa ma'aikaciyar agaji ta kungiyar Red Cross mai suna Hauwa Liman.

Hauwa Mohammed Liman, ma'aikaciyar agaji ta kungiyar Red Cross.
Hauwa Mohammed Liman, ma'aikaciyar agaji ta kungiyar Red Cross. ICRC/Handout via REUTERS
Talla

A watan Maris na shekarar 2018 da muke ciki, mayakan Boko Haram suka sace Hauwa Liman tare da wasu abokan aikinta biyu da kuma wasu mutane, a wani hari da mayakan suka kai kan wani sansanin ‘yan gudun hijira dake Rann hedikwatar Karamar Hukumar Kale Balge a jihar Borno.

Kafin kisan Hauwa Liman, mayakan na Boko Haram sun hallaka abokiyar aikinta Saifura Khorsa a watan Satumba da ya gabata, abinda yasa dubban mutane nuna alhini a ciki da wajen Najeriya.

"Kisan Hauwa ba zai dakushe kokarin ceto wadanda ke hannun Boko Haram ba"

Najeriya: Gwamnati za ta ci gaba da kokarin ceto wadanda ke hannun Boko Haram

A halin da ake ciki dai gwamnatin Najeriya ta bada tabbacin cewa duk da faruwar wannan al’amari, za ta cigaba da tattaunawa da ‘ya’yan kungiyar domin ceto sauran mutanen da ke hannun kungiyar.

Daga Abuja Muhammad Sani Abubakar ya aiko mana da wannan rahoton.

03:09

Rahoto kan kisan ma'aikaciyar agaji ta kungiyar Red Cross Hauwa Liman

Mohammed Sani Abubakar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.