Isa ga babban shafi
Najeriya

NNPC ya kori manajoji 80 bayan sun fadi jarabawa

Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya kori manyan ma’aikatansa masu rike da mukaman manaja har guda 80 bayan sun fadi jarabawar karin girma. 

Ginin Kamfanin NNPC a birnin Abuja
Ginin Kamfanin NNPC a birnin Abuja REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Tun a ranar Jumm’ar da ta gabata Kamfanin ya fara mika takardun sallama ga wadanda al’amarin ya shafa ya kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mai Magana da yawun NNPC, Ndu Ughamadu ya tabbatar da matakin korar manyan jami’an amma ya ce, za a biya su dukkanin hakkokinsu da suke bin kamfanin.

Wata majiya na cewa, matakin sallamar jami’an ya zama dole, domin ci gaba da zamansu zai yi illa matuka ga sauran ma’aikata musamman masu rike da kananan mukamai.

Koda yake wasu bayanai na cewa, Kamfanin ya dauki matakin ne don rage kashe kudade amma ba don inganta tsarin tafiyar da al’amuransa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.