Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun dakile shirin kai hari kan wasu yankunan Zamfara

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Zamfara, ta ce ta yi nasarar dakile yunkurin kai hare-hare kan wasu yankunan jihar, zalika ta kama wani mutum da ake zargin yana cikin wadanda ke yi wa ‘yan bindigar da suka addabi jama’a safarar miyagun makamai.

Wasu jami'an tsaron Najeriya.
Wasu jami'an tsaron Najeriya. AFP
Talla

Yayin zantawa da manema labarai a garin Gusau, kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara, Alhaji Muhammad Zannah, ya ce jami’an tsaron sun dakile yunkurin kai hare-haren ne kan kauyukan Dan-Gamji, Bindin, Gobirawa da kuma Chali, wadanda ke karamar hukumar Maru.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa a lokacin da aka damke Umaru Shehu, wanda ake zargi da yi wa ‘yan bindiga safarar makamai, an same shi dauke da bindigogi 11 kirar gida, kuma ana kan yi masa tambayoyi da zummar gano maboyar wadanda suke taimaka masa.

Rundunar ‘yan sandan da ke Zamfara, ta kuma kama wasu mutane 41, bisa zarginsu da hannu wajen maida zanga-zangar da jama’a suka yi a karamar hukumar Tsafe ranar 24 ga Disamban da ya wuce zuwa tarzoma.

A ranar 24 ga Disamban na 2018, daruruwan mutane suka gudanar da zanga-zanga, a Tsafe, Magazu da Kucheri duka da ke karamar hukumar Tsafe, don nuna bacin ransu kan hare-haren ‘yan bindiga a sassan jihar Zamfara.

Sai dai daga bisani, zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma, lamarin da ya kai ga kone hedikwatar karamar hukumar ta Tsafe, motoci 19, baburan hawa da dama da sauran tarin dukiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.