Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta baiwa APC damar tsaida 'yan takara a Zamfara

Hukumar shirya zaben Najeriya INEC, ta baiwa ‘yan takarar jam’iyyar APC damar shiga zabukan kujerar gwamna da na ‘yan majalisun dokoki na jihar Zamfara.

Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya maizaman kanta INEC.
Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya maizaman kanta INEC. REUTERS/Nyancho NwaNri
Talla

Kwamishinan hukumar ta INEC na kasa, kuma shugaban kwamitin lura da yada labarai da kuma wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yammacin yau.

A cewar INEC, matakin baiwa ‘yan takarar APC damar shiga zabukan jihar Zamfara, ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja, wadda ta bada umarnin a ranar Alhamis 21 ga watan Fabarairu.

A karshen watan Janairu da ya gabata, babbar kotu da ke Gusau a Zamfara da kuma babbar kotun Najeriya da ke Abuja, suka yanke hukunce-hukunce masu cin karo kan makomar APC a jihar ta Zamfara.

Da fari dai babbar kotu da ke Gusau, ta yanke hukuncin tabbatar da zaben fidda gwanin Jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara, wanda ya gudana a ranakun 3 da 7 ga watan Oktoban shekarar 2018, inda kotun ta umarci INEC, da kada a sauya sunayen wadanda suka yi nasara a zaben na fidda gwani.

Sai dai a gefe guda kuma wata babbar Kotu a Abuja ta yanke hukuncin hukumar INEC na da ikon kin karbar 'yan takarar jam'iyyar APC a zabukan na jihar Zamfara saboda gaza kammala zabukanta cikin wa'adin da aka tsara domin zabukan fidda gwanin.

Ranar 10 ga watan Oktoban bara, INEC ta ce, jam’iyyar APC mai mulki ba tada dan takara a matakin jihar Zamfara yayin zabukan 2019, saboda gazawarta wajen kammala zabukan fidda ‘gwani, cikin wa’adin da hukumar ta INEC ta debawa daukacin jam’iyyun siyasar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.