Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Chadi sun shiga Najeriya don yakar Boko Haram

Hukumomin kasar Chadi sun ce yanzu haka dakarun su 500 suka kutsa kai cikin Najeriya domin taimakawa kasar yaki da mayakan kungiyar Boko haram, a daidai lokacin da ake gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu.

Wasu dakarun rundunar sojin kasar Chadi.
Wasu dakarun rundunar sojin kasar Chadi. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Kakakin rundunar sojin Chadi yace sojojin na daga cikin wadanda ke aiki a karkashin rundunar hadin kai da ta kunshi sojojin Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar.

Rahotanni sun ce akalla mutane sama da 200 suka mutu a cikin wannan wata sakamakon hare haren da mayakan book haram suka kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.