Isa ga babban shafi
Najeriya-Rivers

Dubban jama'a sun yi zanga-zanga a Rivers

Dubban Jama’a a jihar Rivers sun gadanar da zanga-zangar adawa da matakin dakatar da tattara sakamakon zaben Gwamna da hukumar INEC ta yi wanda ke zuwa bayan rikice-rikice da zargin magudin zabe a wasu mazabun jihar.

Masu zanga-zanga a garin Fatakwal, kan matakin dakatar da zaben kujerar Gwamnan jihar Rivers.
Masu zanga-zanga a garin Fatakwal, kan matakin dakatar da zaben kujerar Gwamnan jihar Rivers. PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Talla

Matakin dakatar da tattara sakamakon zaben ya zo ne bayan da a ranar Lahadi da ta gabata wasu gungun mutane sanye da kayan soji dauke da makamai suka yiwa cibiyar tattara sakamakon zaben jihar kawanya, tare da neman hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta INEC ta dakatar da aikinta, wanda kuma daga bisani rundunar sojin kasar ta ce ba jami’anta ba ne.

Jihar Rivers mai arzikin man fetur da ke kudancin Najeriya, dai ta yi kaurin suna wajen rikice-rikicen zabe, wanda kuma a wannan karon ya yi kamari.

A jiya Litinin dai dubban magoya bayan jam’iyyar APC mara rinjaye a jihar tare da kungiyoyin fararen hula ne suka gudanar da zanga-zangar don adawa da matakin dakatar da zaben.

Tuni dai gwamnan jihar Nyesome Wike ya zargi hukumar INEC jami’an tsaro da kuma Jam’iyyar APC da yunkurin juya sakamakon zaben.

Zaben na ranar Asabar 9 ga watan Maris wanda ya gudana a jihohi 29 daga cikin 36 da Najeriyar ke da su, na zuwa ne mako biyu bayan babban zaben kasar da shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya samu nasarar zarcewa zuwa zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.