Isa ga babban shafi
Zamfara

'Yan bindiga sun tilasta wa jama'ar Shinkafi kwana a daji

‘Yan bindiga sun tilasta wa jama’ar Karamar Hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara a Najeriya kwana a cikin daji sakamakon farmakin da suka kawo musu a tsakiyar daren da ya gabata, inda suka yi awon gaba da akalla mutane 40 da suka hada da ‘yan kasar Ghana.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 40 a Shinkafi da ke jihar Zamfara a Najeriya
'Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 40 a Shinkafi da ke jihar Zamfara a Najeriya RFI
Talla

Jama’ar yankin sun shaida wa sashen hausa na RFI cewa, sun yi ta kabbara da kiran salla da nufin samun kwarin guiwar tunkarar ‘yan bindigar.

Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi ya bayyana takaicinsa kan yadda jami’an sojoji suka ki kawo musu dauki a yayin hare-haren har sai da 'yan bindigar suka ci karensu babu babbaka.

A cewarsa, daga yanzu babu wani sauran kwarin guiwa da suke da shi akan sojojin Najeriya domin kuwa sun gaza gudanar da ayyukansu na kare rayukan al’ummar yankin.

Dr. Shinkafi ya kara da cewa, daga yanzu za su ci gaba da dogara da kansu wajen samar wa kansu kariya daga ‘yan bindigar saboda jami’an tsaron sun gaza.

"Babu wanda ya yi sahur a cikinmu, amma yanzu mun koma gida domin hutawa, sannan mun umarci matasanmu da su yi gadin jama’a." in ji Shinkafi.

Kuna iya lasta alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da Dr. Sulaiman Shu'aibu Shinkafi.

03:37

Cikakkiyar hira da Dr. Sulaiman Shu'aibu Shinkafi kan harin 'tan bindiga

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.