Isa ga babban shafi
Najeriya

Yara miliyan 8 basa zuwa makarantar boko a Jihohin Najeriya 10 - Rahoto

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF tace yanzu haka yara kanana miliyan 8 ne basa zuwa makarantar boko a Jihohin Najeriya 10 da kuma birnin Abuja.

Yara kanan miliyan 8 basa halartar makaranta a jihohin Najeriya 10.
Yara kanan miliyan 8 basa halartar makaranta a jihohin Najeriya 10. UNICEF
Talla

Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar domin tuna ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin ‘Yaran Afirka’.

Sanarwar da wakilin hukumar UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins ya fitar ta bayyana Jihohin dake fama da wannan matsala da suka hada da Bauchi da Niger da Katsina da Kano da Sokoto ad Zamfara da Kebbi da Gombe da Adamawa da kuma Taraba.

Hawkins yace yanzu haka wasu matasa 2,000 sun sanya hannu akan takardar korafi da suke bukatar shugabannin dake jagorancin wadanan jihohi guda 10 sun tabbatar da bada ilimi mai inganci da wadannan yara da basu zuwa makaranta musamman matan dake cikin su.

Jami’in yace tashe tashen hankulan da ake samu a yankin arewacin Najeriya ya hana yara miliyan 10 da rabi samun ilimi mai inganci, yayin da rikicin book haram ya haifar da lalata makarantu da kashe malamai da kuma tsorata iyaye tura yaransu zuwa makaranta.

UNICEF ta bukaci kaddamar da shiri na musamman da zai inganta makarantu da samar musu da tsaron da ya dace, domin baiwa iyaye karfin gwuiwar tura ‘yayan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.