Najeriya ce kasa ta 2 a duniya inda ake aurar yara mata - UNICEF
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce kasa ta biyu a duniya da ake aurar da yara mata masu karancin shekaru.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Asusun na UNICEF ya ce kididdiga ta nuna cewar, kananan yara mata akalla miliyan 23 aka aurar a kasar, wanda hakan ya kawo karshen ci gaban karatunsu.
Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ya nuna cewar adadin kananan yara mata da aka aurar a duniya ya kai kusan miliyan 650.
Babban jami’in asusun na UNICEF a Najeriya Bhanu Pathak, ya bayyana hakan a garin bauchi, yayin bikin cika shekaru 30 da kafa hukumar kare hakkin kananan yara ta duniya CRC, da ya gudana a jihar Bauchi.
Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar a baya bayan nan ya nuna cewar adadin kananan yara mata da aka aurar a duniya ya kai kusan miliyan 650.
Zalika rahoton ya yi hasashen cewa akwai fargabar aurar da karin wasu kananan yaran miliyan 150, nan da shekara ta 2030.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu