Isa ga babban shafi
Najeriya

Al'ummomin Bayelsa da Kogi na kada kuri'a a zaben gwamnoni

Yau ake zaben gwamnoni a jihohin Kogi da kuma Bayelsa a Najeriya, inda rundunar ‘yan san dan kasar ta aike da jami’anta dubu 66 da 241, don tabbatar da doka da oda.

Wani jami'in zabe a Najeriya rike da takardar kada kuri'a.
Wani jami'in zabe a Najeriya rike da takardar kada kuri'a. eNCA
Talla

Daga cikin wannan adadi dai, rundunar ‘yan sandan tace dubu 35 da 200 an girke su ne a jihar Kogi, yayinda aka tura dubu 31 da 41 zuwa Bayelsa.

A Bayelsa ‘yan takara 45 ke fafatawa, inda ke sa ran hamayya za ta fi zafi tsakanin dan takarar PDP Douye Diri da Mista David Lyon na jam’iyyar APC. Yayinda a Kogi ‘yan takara 24 za su fafata, ciki har da gwamna mai ci Yahya Bello na APC da kuma dan takarar PDP Musa Wada.

Gabannin zaben na yau, a jiya Juma’a wasu ‘yan bindiga suka yi yunkurin kutsawa wani Otal a garin Lokoja, masaukin gwamnan jihar Oyo Sheyi Makinde, wanda ke jagorantar yakin neman zaben jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Kogi.

Sai dai jami’an tsaron da kuma taimakon jama’a sun dakile yunkurin, kawo yanzu kuma babu karin bayan kan ko an kai ga kamen wadanda ake zargi da hannu wajen kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.