Isa ga babban shafi

Kotu ta soke sabbin masarautun jihar Kano

Babbar Kotun Jihar Kano dake Najeriya ta soke sabbin Masarautu guda 4 da Gwamnatin Jihar ta kirkiro.Alkalin kotun Usman Na’Abba ya yanke hukuncin cewar Majalisar dokokin Jihar Kano bata bi matakan da suka dace ba wajen amincewa da kudirin kirkiro sabbin Masarautun, wadanda jama’a da dama ke kallon su a mtsayin yunkurin rage tasirin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.Wannan ya sa mai shari’ar ya yanke hukuncin soke Masarautun guda 4 da suka hada da na Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye da kuma Sarakunan da aka nada.Masu sharhi na kallon wannan hukunci a matsayin nasara ga Sarki Sanusi wanda ake zargin sa da sukar wasu manufofin gwamnatin jihar wadanda yace kan sabawa manufofin cigaban jihar.Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don sauraron rahoto akai..

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu kan rakumiyayin hawan daushe na babbar sallah,inda ya karbi bakwancin shugaban kasar Guenea Alpha Conde
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu kan rakumiyayin hawan daushe na babbar sallah,inda ya karbi bakwancin shugaban kasar Guenea Alpha Conde Aminiya|rfi
Talla
01:28

Kotu ta sauke sabbin masarautun jihar Kano

Abubakar Dangambo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.